Ƙungiyar ASSOMEG ta taya Abba Kabir Yusuf murnar samun nasara a kotun ƙoli

0
117

Kungiyar kafafen yaɗa labarai ta yanar gizo Association of Online Media Guild, ta taya gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano murnar samun nasara a kotun ƙoli.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta raba wa manema labarai ta hannun shugabanta na riko, Abdullateef Abubakar Jos.

A ranar Juma’a nan ne dai kotun ƙoli ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan Jihar Kano bayan da kotun sauraren ƙararrakin zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka soke nasarar sa.

KU KUMA KARANTA: Kotun Ƙoli ta tabbatar da Dauda Lawan a natsayin gwamnan jihar Zamfara

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnan jihar da ya kiyaye kyakkyawar alaƙar da yake da ita da ’yan jarida na yanar gizo, domin Kano ce ta biyu da ta ke da ɗimbin masu kafafen yaɗa labarai na yanar gizo baya ga jihar Legas.

A ƙarshe ƙungiyar ta buƙaci Gwamnan da ya ƙara inganta ayyukan more rayuwa domin cigaban jihar Kano.

Leave a Reply