No menu items!

Sample Page Title

Date:

Allah Ya yi wa mai magana da yawun Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum rasuwa.

Malam Isa Gusau ya rasu ne a wani asibiti a ƙasar Indiya a jiya Alhamis, inda ya yi doguwar jinya kamar yadda wakilinmu ya ruwaito.

Malam Isa Gusau, ya riƙe muƙamin mai magana da yawun tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima, wanda a yanzu shi ne Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya.

Bayanai sun ce Malam Isa Gusau ya kwashe sama da wata guda yana jinya a wani asibiti a Indiya.

Majiyar ta ce: “mun rasa Gusau da sanyin safiyar ranar Alhamis inda ya yi kusan kwana uku a sume kafin rasuwar sa.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa, ta je ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar mawallafin jaridar Neptune Prime

“Duk mun yi masa addu’ar samun lafiya, amma Allah bai yarda kuma Ya karɓi abinsa kasancewar Ya fi mu sonsa.”

Makusanta da ke ci gaba da alhini sun bayyana marigayi Isa Gusau a matsayin mutumin kirki da taka-tsan-tsan kan harkokin rayuwa wajen ganin ya sauke nauyin duk wanda ya rataya a wuyansa.

Har yanzu dai ba a bayyana lokacin da za a dawo da gawarsa gida Najeriya ba domin yi masa jana’iza.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...