Guinea ta takaita sadarwar intanet saboda matsalar tsaro

0
129

Ministan harkokin wajen Guinea ya shaida wa jami’an diflomasiyya cewa tsaikon da ake samu a kan intanet a ƙasar na faruwa ne saboda wata matsalar tsaro, a wani jawabin da aka watsa a gidan talabijin na ƙasar.

Kimanin jakadun ƙasashe 15 ko wakilansu ciki har da wakilai daga ƙungiyar Tarayyar Turai da Amurka da China ne suka gana da Morissanda Kouyate domin kokawa kan rashin ingancin intanet, kamar yadda jawabin da aka watsa ranar Laraba da maraice ya nuna.

Sun koka a kan keta ‘yancin faɗar albarkacin baki da rashin samun intanet da rashin man fetur bayan an yi mummunar gobara a babban wurin ajiyar fetur a ƙasar a watan Disamba da kuma matsalolin da ke fuskantar ma’aikatansu.

An kwashe makonni ana fama da matsanancin rashin intanet a Guinea, wadda sojojin da suka yi juyin mulki a shekarar 2021 suke mulka.

KU KUMA KARANTA: Muna ƙoƙarin kakkaɓe matsalar tsaro amma har yanzu ba mu yi nasara ba — Tinubu

Mahukunta kuma sun sanya sharuɗɗa kan kafafen watsa labarai masu zaman kansu yayin da aka katse kafafen sada zumunta da kuma gidajen rediyo masu zaman kansu tare da shafukan intanet na jaridu sannan ake kamawa ko far wa ‘yan jarida.

“Ta shafi dukkanmu, wata matsalar tsaro ta shafe mu,” in ji Kouyate a cikin jawabin da ya yi a talabijin.

Bai ba da ƙarin bayani ba game da matsalar. “Ba za mu iya ƙara bayani a kai ba,” in ji shi.

Ministan na harkokin waje ya kuma shaida wa jami’an diflomasiyya cewa matsalolin da ofisoshin jakadancinsu ke funkanta sun shafi ma’aikatan ƙasar Guinea ma.

“Game da matsalar sadarwa, akwai wannan matsalar a fadar shugaban ƙasa,” a cewarsa, yana mai ƙarawa da cewa za su warware matsalar nan ba da jimawa ba.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta koka a ƙarshen watan da ya gabata game da “ƙaruwar take ‘yancin ‘yan jarida ” a Guinea kuma ta yi ƙira ga hukumomi su sauya yanayin nan-take.

Kanar Mamady Doumbouya, shugaban gwamnatin mulkin soja ta ƙasar, ya yi alƙawarin miƙa mulki ga farar-hula a watan Janairun shekarar 2026.

Leave a Reply