Connect with us

Ƙasashen Waje

Amurka da Birtaniya sun ƙaddamar da hare-hare kan ‘yan tawayen Houthi na Yemen

Published

on

Sojojin Amurka da na Birtaniya sun kai hare-hare a yankunan ‘yan tawayen Houthi na Yemen, inda suka yi amfani da jiragen ruwan yaƙi wurin harba makamai masu linzami samfuran Tomahawk tare da jiragen sama na yaƙi.

Sojojin sun kai hare-hare a wuraren da suka haɗa da ma’ajiyar makamai da na’urorin kare hare-hare ta sama, a cewar jami’an gwamnatin Amurka ranar Juma’a da safe.

Waɗannan hare-hare su ne karon farko da Amurka ta yi martani kan ‘yan tawayen Houthi waɗanda suka daɗe suna yin amfani da jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami wajen kai hari kan jiragen ruwa na ɗaukar kaya da ke zuwa Isra’ila tun lokacin da aka ƙaddamar da hare-hare a Gaza.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce hare-haren da suka kai Yemen sun nuna cewa ƙasarsa da ƙawayenta ba za su “lamunci” hare-haren da ‘yan tawayen Houthi suke kai wa jiragen ruwansu ba.

KU KUMA KARANTA: Biden ya ce Amurka ba za ta bari a tursasa wa Falasɗinawa fita daga Gaza ba

A wata sanarwa da ya fitar, Biden ya ce a karon farko sun yi amfani da makamai masu linzami na ruwa wajen kai hare-hare kan ‘yan tawayen Houthi domin yin raddi game da jerin hare-haren da suke kai wa jiragen ruwa da ke wucewa ta Bahar Maliya.

A gefe guda, shugaban Houthi Ali al-Qahoum ya ce sun ƙaddamar da hare-hare kan jiragen yaƙin Amurka da Birtaniya da ke Bahar Maliya domin yin martani kan hare-haren da aka kai musu.

“Amurkawa da Masu kishin Yahudawa da Birtaniya da ke yaƙi da Yemen sun ƙaddamar da jerin hare-hare a babban birnin, Sanaa, da yankin Hudaida da Saada, da kuma Dhamar,” a cewar wani jami’in Houthi Abdul Qader al Mortada a sakon da ya wallafa a shafin X.

Wakilan kamfanin dillancin labarai na Associated Press journalists a Sanaa sun ce sun ji ƙara huɗu ta fashewar wasu abbuwa amma ba su ga alamar jiragen yaƙi ba.

Mutum biyu mazauna Hudaida, Amin Ali Saleh da Hani Ahmed, sun ce sun ji ƙara guda biyar ta fashewar bama-bamai. Hudaida yanki ne da ke tsakanin Bahar Maliya kuma shi ne birni mafi girma mai tashar jiragen ruwa da ke ƙarƙashin Houthi.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu

Published

on

Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu

Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu

Daga Ibraheem El-Tafseer

Frane Selak ya kasance wanda ya fi kowa tsallake rijiya da baya a duniya.

A shekarar 1962 ya tsallake haɗarin jirgin ƙasa wanda mutane 17 suka mutu, a 1963 jirgi ya faɗi da shi kowa ya mutu sai shi kaɗai ko ƙwarzane bai yi ba.

A shekarar 1966 motar safa ta lume da su a rafi mutum huɗu sun mutu amma Frane bai samu ko ƙwarzane ba a yayin da a shekarar 1973 motarsa ta kama da wuta ya tsallake rijiya da baya, ya kuma tsallake haɗarin taho mu gama da mota ta yi da shi ya tsira ya kuma lashe yuro dubu ɗari takwas a Caca a shekarar 2003.

KU KUMA KARANTA: Labarin zuwa Hajji mai ban mamaki

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Published

on

Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza, inda ta tilasta wa ɗaruruwan Falasɗinawa tserewa bayan da soji suka kuma ba da umarnin ƙaurace wasu yankuna masu yawan jama’a.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Isra’ila sun ce an yi musayar wuta da dakarun Masar

Waɗanda suka shaida lamarin sun ce an kai hari da dama a ciki da wajen birnin Khan Younis, inda aka hallaka mutane takwas kuma mutane sama da 30 suka samu raunuka, cewar wata majiyar lafiya da kuma ƙungiyar Red Crescent ta Falasɗinawa.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana – COPEC

Published

on

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana - COPEC

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana – COPEC

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Man Fetur a Ghana ta yi hasashen cewa akwai yiwuwar a samun ƙarin farashin man fetur a ƙasar a farkon watan Yulin 2024.

Ƙungiyar ta Chamber for Petroleum Consumers (COPEC) ta ce akwai alamu masu ƙarfi da ke nuna cewa farashin fetur da man dizel da gas zai ƙaru baki ɗaya a gidajen man da ke faɗin ƙasar, kamar yadda kamfanin watsa labarai na ƙasar Ghana ya ruwaito.

COPEC ɗin ta ce za a samu ƙarin farashin ne sakamakon yadda farashin Cedi ɗin a ƙasar ke ƙara karewa idan aka kwatanta da dalar Amurka.

COPEC ɗin ta yi hasashen cewa farashin man fetur ɗin wanda za a rinƙa sayarwa a gidan mai zai ƙaru da kashi 2.17 cikin 100, wanda hakan ke nufin zai ƙaru daga Cedi 14.17 zuwa Cedi 15.20 a duk lita.

Sai kuma farashin dizel ana sa ran ya ƙaru zuwa 15.21 a kowace lita ɗaya, sai kuma na gas ya koma tsakanin Cedi 13.24 zuwa Cedi 14.64 a duk kilo ɗaya.

KU KUMA KARANTA: Ɗan Ghana ya kafa tarihi na rungumar bishiyoyi a duniya

Ƙungiyar ta COPEC ta bayar da shawara ga gwamnatin Ghana da ta yi duk mai yiwuwa domin rage harajin da yake a kan gas ko kuma yin tallafi a farashinsa domin bayar da dama ga ‘yan ƙasar su same shi a farashi mai rahusa.

Ta kuma yi ƙira ga gwamnati da kada ta yi ƙasa a gwiwa wajen dawo da matatar mai ta Tema a kan aiki (TOR) don kaucewa ko kuma rage shigo tattacen man fetur wanda a wani lokacin ake samun gurɓatacce.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like