No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gargaɗi ‘yan Najeriya da ka da su yi amfani da wata sabuwar sara da ta fito, “No dey gree for anybody”

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ACP Muyiwa Adejobi, ne ya yi wannan gargaɗin yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja a ranar Laraba.

Ya ce, “Sabuwar sarar ta 2024 ga matasan mu ita ce; “No dey gree for anybody.”

“A cewar bayanan sirrinmu, taken yana fitowa ne daga wani ɓangare na juyin juya hali wanda zai iya haifar da matsaloli a faɗin ƙasar.

“Babu yarda ga kowa” ana ɗaukarsa a zaman wata sara, amma a cikin duniyar tsaro, muna kallonsa a matsayin kalma mai haɗari wacce zai iya haifar da rikici.”

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...