Masarautar Fika, Pataskum da Tikau sun je ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar mawallafin jaridar Neptune Prime

0
144

Daga Ibraheem El-Tafsser

Mai Martaba Sarkin Fika, kuma shugaban sarakunan jihar Yobe, Alhaji Muhammad Abali Ibn Muhammad Idris, ya aika Alhaji Ali Adamu Fika ya wakilce shi a wajen ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar Dakta Hassan Gimba (mawallafin jaridar Neptune Prime) a gidansu da ke garin Potiskum jihar Yobe, a yau Laraba.

Alhaji Ali ya yi addu’o’i na musamman da fatan Allah jiƙanta da rahama, ya gafarta mata.

Haka kuma Mai Martaba Sarkin Pataskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, ya aiko da tawaga ta musamman daga fadarsa domin ta’aziyyar rasuwar Hajiya Hafsat Ahmed.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya je ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar mawallafin jaridar Neptune Prime

Mai Martaba Sarkin Tikau, Alhaji Muhammad Abubakar Ibn Grema, shi ma ya turo tawaga ta musamman daga fadarsa da ke ƙaramar hukumar Nangere, domin yi wa Dakta Hassan Gimba ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa.

Jama’a da dama ne suke ta tururuwa zuwa yi masa ta’aziyya. Ciki har da Hakimin Kukuri, Sardaunan Fika, Alhaji Audu Babayo, tsohon ɗan majalisar dattijai da Alhaji Adamu Gwargwar. Sannan akwai tawaga ta musamman daga makarantun CAMTECH da FCE Potiskum.

Sannan a yau ne aka yi addu’ar uku na rasuwar Hajiya Hafsat Ahmed.

Leave a Reply