No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Ibraheem El-Tafsser

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, ya je ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar mawallafin jaridar Neptune Prime Dakta Hassan Gimba, a gidansu da ke garin Potiskum jihar Yobe.

Gwamnan Yobe, wanda mataimakinsa Alhaji Idi Barde Gubana (Wazirin Fune) ya wakilce shi, ya bayyana rashin Hajiya Hafsat Ahmed, a matsayin babban rashi, ba ga ‘ya’yanta kaɗai ba, ga dukkan al’ummar musulmi.

KU KUMA KARANTA: Mahaifiyar Mawallafin Neptune Prime, Hassan Gimba, ta rasu tana da shekara 85

Hajiya Hafsat wadda ta rasu ranar Talata, ta rasu tana da shekaru 85. Ta bar ‘ya’ya tara da jikoki da ‘ya’yan jikoki 77.

Ya yi addu’ar Allah ya jiƙanta da rahama, ya gafarta mata.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...