‘Yan Boko Haram sun kai sabon hari a Borno, sun ƙona mutane da ransu

0
157

Ƴan ta’addan Boko Haram sun kai sabon harin ta’addanci a garin Gajiram da ke ƙaramar hukumar Nganzai ta jihar Borno.

Mutum shida ne suka ƙone ƙurmus yayin da wasu mutum huɗu suka samu raunuka daban-daban a harin da ƴan ta’addan suka kai da yammacin ranar Litinin, 8 ga watan Janairun 2024, Legit Hausa ya wallafa.

Majiyoyi waɗanda suka tabbatar wa jaridar Leadership harin ranar Talata a Maiduguri, babban birnin jihar, sun ce lamarin ya faru ne bayan sallar Magariba a wata unguwa da ke kusa da wata kasuwa a garin na Gajiram.

Ɗaya daga cikin majiyoyin ya bayyana cewa: “An kashe mutum shida a jiya bayan sallar Magriba a Gajiram. Mutum huɗu sun samu raunuka. An kai harin ne a wata unguwa da ke kusa da kasuwar garin.”

Rundunar soji da kuma rundunar ƴan sandan jihar Borno ba su fitar da wata sanarwa dangane da faruwar lamarin ba har zuwa lokacin fitar da wannan rahoton.

Rahoto ya zo cewa wasu matafiya mutum takwas sun rasa rayukansu bayan bam ya tashi da motocinsu suna tsaka da tafiya a jihar Borno.

KU KUMA KARANTA: ’Yan Boko Haram sun kashe ɗan sanda a tawagar gwamnan Yobe

Matafiyan dai na kan hanyarsu ne ta zuwa Dikwa daga Ngala lokacin da bam ɗin ya tashi da su. Mutane da dama sun samu munanan raunuka yayin da motocin suka yi lalacewar da ba za su gyaru ba.

Leave a Reply