’Yan bindiga sun dawo hanyar Abuja-Kaduna, sun sace matafiya 30

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi a Dogon-Fili kusa da Katari a ƙaramar hukumar Kachia a Jihar Kaduna.

Karo na farko ke nan cikin fiye da wata 10 da mahara suka sace jama’a a kan titin Abuja zuwa Kaduna.

Binciken Aminiya ya nuna cewa hari na karshe da aka kai a kan titin shi ne na ranar 1 ga watan Maris, 2023, wanda da aka sace mutum 23.

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya sanar a shafinsa na X cewa abokansa biyu daga ’yan siyasa sun tsallake rijiya da baya a harin na ranar Lahadi.

Ya ce ’yan bindigar sun ci karensu babu babbaka na tsawon lokaci duk da cewa an girke jami’an tsaro a kan babar hanyar.

Shehu Sani ya ce, “A daidai lokacin da muke tunanin mun samu kwanciyar hankali, a daren jiya (Lahadi) ’yan bindiga sun kai hari, sun dawo hanyar Kaduna-Abuja.

“Sun tare hanyar da misalin karfe 9 na dare inda suka sace mutane masu yawa a kusa da ƙauyen Katari.

“Abokaina biyu, ɗan jam’iyya mai mulki da ɗan adawa sun tsere daji kamar Usain Bolt.

KU KUMA KARANTA: ’Yan bindiga sun kashe ɗan uwan amarya, sun sace mahalarta biki a Kaduna

“Amma duk da an inganta tsaro a kan hanyar fiye da yadda yake a baya.”

Wani mazaunin Katari, Suleiman Dan Baba, ya ce da misalin ƙarfe 9:33 na dare ne ’yan bindiga ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 suka fito daga daji suka tare kowane ɓangaren titin kuma sun ɗauki tsawon minti 45 a kan hanyar.

Suleiman ya ce maharan sun buɗe wa motocin matafiya wuta, suka fasa musu tayoyi, wanda hakan ya sa dole suka tsaya.

“’Yan bindigar sun tilasta wa matafiya fita daga motocinsu da bakin bindiga, suka wuce da su cikin daji,” in ji shi.

Wani mazaunin garin Jere, Samaila Shehu, ya ce lamarin ya faru ne da nisan kimanin kilomita daya daga garinsu, kuma an sace matafiya sama da 30 a wurin.

‘Yan bindigar sun raba kan su gida biyu, inda ɗaya tsagin suka kai farmaki ƙauyukan Bishini da Kokore da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, ɗaya tsagin kuma suka yi awon gaba da matafiya da ba a tantance adadinsu ba.

Wani shugaba a yankin Jere, Shu’aibu Adamu Jere, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa ɗan uwansa ya kuɓuta daga harin na kusa da Katari a ranar Lahadi.

Ya ce an jikkata wani direba, sannan an gano motoci biyu, ƙirar Sharon da wata ƙaramar mota a bakin hanya babu kowa a cikinsu bayan harin.

“Eh, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare, kuma sun dauki tsawon minti 45 a kusa da Dogon Fili da ke kusa da Katari a ranar Lahadi.

“An harbi wani direban ɗaya daga cikin motocin kuma aka bar shi a wurin. Akwai wani ɗan uwana da ya tsira daga harin,” in ji shi.

Sai dai ya kasa bayyana adadin mutanen da aka sace a harin, amma ya ce an garzaya da direban da ya jikkata zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba domin yi masa magani.

Shi ma wani mazaunin Katari, wanda lauya ne amma ya buƙaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa an tare hanyar a daren Lahadi a lokacin da yake shirin komawa Kaduna.

A cewarsa, sojojin da ke da nisan mil 500 daga Katari sun fatattaki ’yan bindigar.

“An faɗa min cewa ’yan bindiga sun tare hanya a daren kafin sojoji da ke Katari su zo zu fatattake su. Amma ban sani ba ko an sace mutane,” in ji shi.

Da aka tuntuɓi kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce ba zai iya tabbatar da faruwar lamarin ba.

Shi ma kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, da aka tuntube shi, ya ce zai bincika dom tabbatar da gaskiyar lamarin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *