Mahaifiyar Mawallafin Neptune Prime, Hassan Gimba, ta rasu tana da shekara 85

0
158

Hajiya Hafsat Gimba Ahmed, mai shekaru 85, mahaifiyar Dr. Hassan Gimba, wacce ya kafa, kuma mawallafin Neptune Prime, ta rasu.

Ta rasu ne da sanyin safiyar ranar Litinin a asibitin ƙwararru na Potiskum dake jihar Yobe.

Barista Suleiman Hassan Gimba, wanda ya tabbatar da wannan labari mai ban tausayi a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa za a yi sallar jana’izar da misalin karfe 4:00 na yamma a fadar Sarkin Fika.

Marigayiya Hajiya Hafsat, ta rasu ta bar ‘ya’ya tara da jikoki da dama. A ranar Lahadi da daddare ta yi rashin lafiya, inda ta samu kulawar likitoci, daga bisani kuma ta rasu.

Allah Ya jikan ta da Rahama

Leave a Reply