‘Yan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 43 da laifin kashe matarsa a Yobe

0
129

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta ce ta kama wani mutum mai suna Abubakar Musa mai shekaru 43 da haihuwa da laifin mutuwar matarsa Ammi Mamman a Damaturu.

DSP Dungus Abdulkarim, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Damaturu ranar Juma’a, inda ya ce lamarin ya afku ne a unguwar New Bra-Bra Estate da misalin karfe 4:48 na safiyar ranar Alhamis.

Abdulkarim ya ce wanda ake zargin suna kan gado ɗaya da matar ne a lokacin da aka caka mata wani abu a wuyanta, wanda ya yi sanadin zubar da jini mai yawa wanda ya kai ga mutuwarta.

KU KUMA KARANTA: An kashe wani mutum da rana tsaka a gaban iyalinsa a Kebbi

Ya ce jami’an tsaro na ‘yan sanda suna yi wa mutumin tambayoyi domin bayyana al’amuran da suka shafi mutuwar matarsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya yi ƙira ga duk wanda ke da sahihin bayani kan lamarin da ya fito domin tabbatar da adalci ga wanda ake zargi da kuma wacce ta rasu.

Leave a Reply