Wani saurayi ya chaka wa liman wuƙa saboda ya hana shi shan tabar wiwi a kusa da Masallaci

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wani kasurgumin ɗan daba mai suna Yusuf Haruna AKA Lagwatsani mai shekaru 18 bisa laifin kashe wani fitaccen limami mai suna Malam Sani Mohammed Shuaibu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Kiyawa Haruna, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba, 3 ga watan Janairu, 2024, ya ce Haruna, na karamar hukumar Dala ta jihar, ya daɓa wa malamin wuƙa har lahira bayan marigayin ya yi ƙoƙarin hana shi da ’yan ƙungiyarsa shan tabar wiwi a kusa da harabar Masallacin.

 “A ranar 31/12/2023 da misalin karfe 1930 ne aka samu rahoto daga wani Musa Yunusa ‘m’ na Jakara Quarters Kano cewa a ranar da misalin ƙarfe 1900, Yusuf Haruna ya kai hari tare da daɓa wa wani Malam Sani Mohammed Shuaibu mai shekaru 45 wuƙa mai kaifi a bayansa yayin da yake alwala, kawai saboda wanda abin ya shafa ya gargaɗe shi da ‘yan ƙungiyarsa da su daina shan tabar wiwi a kusa da harabar Masallacin,” in ji sanarwar.

KU KUMA KARANTA: An yi wa Alkali dukan kawo wuka a Gombe

“Saboda haka, wanda abin ya shafa ya samu rauni sosai, aka garzaya da shi asibitin ƙwararru na Murtala Muhammed, kuma likita ya tabbatar da mutuwarsa.

“Lamarin ya girgiza al’umma, kuma jami’an mu sun yi bakin ƙoƙarinsu wajen zaƙulo maharin tare da kama shi.  Wannan kamun ya shaida mana jajircewarmu na kare martabar rayuwa da kuma tabbatar da adalci ga waɗanda irin waɗannan munanan ayyuka suka shafa.”

PPRO ya ƙara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel, ya baiwa jama’a tabbacin hukumar ta ɗau alwashin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

“Bugu da ƙari, za mu yi aiki tuƙuru don tattara ƙwararan hujjoji don tabbatar da nasarar gurfanar da mutanen da aka kama.”

“Manufarmu ba wai kawai mu gurfanar da waɗanda suka aikata laifin a gaban ƙuliya ba ne, har ma da zama kange ga wasu da za su yi tunanin irin wannan aika-aikar.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *