Majalisun Dokokin Najeriya sun amince da naira tiriliyan 28.77 a matsayin kasafin kuɗin 2024

0
144

Majalisun dokokin Nijeriya, Majalisar Dattawa da ta Wakilai, sun amince da naira tiriliyan 28.77 a matsayin kasafin kuɗin 2024 ranar asabar, bayan sun ƙara yawan kuɗin da ƙasar za ta kashe a shekarar.

‘Yan majalisun dokokin sun ƙara naira tiriliyan 1.2 a kan naira tiriliyan 27.5 da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya gabatar musu ranar 29 ga watan Nuwamba.

Sun yi ƙarin ne sakamakon ƙorafin da ma’aikatun gwamnati suka yi na rashin isassun kuɗi a kasafin da shugaban ƙasar ya gabatar da kuma buƙatar da shugaban ya miƙa musu ta ƙara yawan kasafin kuɗi saboda yadda darajar naira ke ci gaba da raguwa.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin 2024

Kasafin kuɗin da aka yi wa kwaskwarima a takaice:

Jumullar kasafin kuɗin 2024 – naira tiriliyan 28.77

Manyan ayyuka – naira tiriliyan 8.7

Ayyukan yau da kullum – naira tiriliyan 9.99

Biyan Bashi – naira tiriliyan 8.27

Sauyin dala – Kasafin ya dogara ne a kan sauya duk dala daya a kan naira 800.

Tinubu ya ce zai mayar da hankali a kan harkokin tsaro da noma da sufuri, da kiwon lafiya, da dai sauran muhimman sassa, a kasafin kuɗin, wanda shi ne na farko da ya gabatar a matsayin shugaban ƙasa.

Leave a Reply