Gwamnonin da suka rasu a kan mulki a Najeriya

0
245

Rasuwar Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu a safiyar Laraba, ta dawo wa ’yan Najeriya da juyayin sauran gwamnoni da suka gamu da ajalinsu a lokacin da suke kan karaga mulki.

Kafin Akeredolu akwai wasu gwamnoni uku da suka riga mu gidan gaskiya a lokacin da suke kan karagar mulki.

1- Shehu Kangiwa:

Shehu Kangiwa

Gwammnan Jihar Sakkwato Shehu Kangiwa  shi ne ya fara rasuwa akan mulki.

Gwamna Shehu Kangiwa ya rasu ne bayan da ya faɗo daga kan doki a lokacin da yake buga wasan Polo a watan Nuwamban 1981.

Daga bisani aka rantsar da mataimakinsa, Garba Nadama a matsayin gwamnan jihar, har zuwa watan Nuwamba 1983 da Muhammadu Buhari ya yi juyin mulki da karfin soji.

2- Mamman Bello Ali:

Mamman Bello Ali

Gwamnan Yobe da ya rasu ne a shekarar 2009 a sakamakon cutar Leukemia, sakanarar ɓargo.

Gwamna Mamman Bello Ali ya rasu ne a zangon farkon mulkinsa na farko a ƙasar Amurka, inda yake duba lafiyarsa.

Bayan nan ne aka rantsar da mataimakinsa, Bukar Abba Ibrahim a matsain sabon gwamnan jihar.

3- Patrick Ibrahim Yakowa:

Patrick Yakowa

Gwamnan Kaduna da ya rasu a zangon farko na mulkinsa a 2012 a hasarin jirgin sama, bayan shekara biyu da ransar da shi.

Likkafar Yakowa wanda mataimakin gwamnan Kaduna ne ta daga ne ne bayan Gwamna Muhammad Namadi Sambo ya samu ɗaukaka zuwa mataimakin shugaban ƙasa bayan Goodluck Jonathan ya gaji kujerar shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Aduwa, wanda ya rasu a sakamakon rashin lafiya.

Yakowa ya gamu da ajalinsa ne a hanyarsa ta Fatakwal daga Jihar Baelsa inda suka halarci jana’izar mahaifin Oronto Douglas.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, ya rasu

Helikwaftan da suke ciki tare da tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Janar Andrew Owo Azazi ne ya yi hatsari kuma babu wanda ya tsira.

A cikin jirgin akwai hadimansa guda biyu Dauda Tsoho da Mohammed Kamal da kuma mauka jirgin biyu Murtala Mohammed Daba da Adeyemi Sowole.

Bayan nan ne aka rantsar da mataimakinsa, Mukhtar Ramalan Yero.

4- Rotimi Akeredolu:

Rotimi Akeredolu

Gwamnan Ondo da ya rasu ranar 27 ga Disamamba, 2023 sakamkon rashin lafiya a zango na biyu na mulkinsa.

Rashin lafiyar ta sa shi mika ragamar jihar ga mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa na kusan wata shida, tun daga lokacin da ya je duba lafiyarsa a ƙasar Jamus a watan Yuni.

Leave a Reply