Rasha ta sake buɗe ofishin jakadancinta a Burkina Faso bayan shekara 30

0
258

Ƙasar Rasha ta sake buɗe ofishin jakadancinta a Burkina Faso a ranar Alhamis bayan shafe kusan shekaru 32, a cewar sanarwar gwamnatin ƙasar da ke yankin Afirka ta Yamma da kuma jami’in diflomasiyyar Rasha suka fitar.

An rufe ofishin ne a shekarar 1992, a cewar Jakadan Rasha a makwabciyar kasar Ivory Coast Alexei Saltykov, shugaban Rasha Vladimir Putin zai nada sabon jakadan Rasha a Burkina Faso.

A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Burkina Faso ta fitar ta tabbatar da cewa “Rasha ta sake buɗe ofishin jakadancinta a yau Alhamis a Ouagadougou.”

Saltykov ya ce zai jagoranci ayyukan diflomasiyyar Rasha a Burkina Faso har sai an nada sabon jakadan, yana mai bayyana Burkina Faso a matsayin “tsohuwar abokiyar hulda da muke da kyakkyawar alaƙa ta abota.”

KU KUMA KARANTA: Yukiren ta ce ta kakkaɓo jirage marasa matuƙi na Rasha sama da 70

A bara Burkina Faso ta fuskanci juyin mulkin soji har sau biyu — sun samo asali ne sakamakon rashin gamsuwa da kuma gazawar da aka yi wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro ta masu tada ƙayar baya.

Tun bayan hawan su mulki a watan Satumban 2022, gwamnatin mulkin sojin kasar ta nesanta kanta daga Faransa, daɗaɗɗiyar abokiyar huldarta, sannan wacce ta mata mulkin mallaka, kana ta matsa kusa da Rasha.

A watan Oktoba ne Burkina Faso ta ƙulla yarjejeniya da ƙasar Rasha kan gina tashar makamashin nukiliya domin ƙara samar da makamashi a yankin Sahel inda ƙasa da kashi ɗaya cikin huɗu na al’ummar ƙasar ke samun wutar lantarki.

Leave a Reply