Wani soja a Borno ya kashe direban kayan agaji kan na-goro

Wani soja ya kashe direban motar kayan agaji da saboda ƙin ba shi na-goro a hanyar Dikwa zuwa Gamboru da ke Jihar Borno.

A safiyar Alhamis ce Sakataren Ƙungiyar Ma’aikatan Sufurin (NURTW) Ahmed Musa ya sanar cewa direban da sojan ya kashe na ɗauke da kayan agaji ne zuwa N’djamena na Jamhuriyar Chadi.

Musa ya tabbatar cewa direban ya samu izini daga hedkwatar sojoji da kwamandan rundunar Operation Haɗin Kai na Arewa maso Gabas, amma duk da haka sojan da ke wani shingen binciken ababen hawa ya nemi ya ba shi kuɗi.

“Amma ya bayyana wa sojan cewa kayayyakin jinkai ne a cikin motar kuma kwamandan rundunar ya sahale musu, inda  ya ba da takardar izinin.

KU KUMA KARANTA: Budurwa ta yi amfani da bindigar ɗan sanda ta harbe shi har lahira

Duk da haka, sojan ya yi watsi da takardun ya lakaɗa wa direban da yaronsa duka da kotar bindiga, har sai da direban ya suma, daga baya ya ce ga garinku nan.

“Haka muke rasa direbobi a sakamakon zaluncin da sojoji a hanyar Gambarou, shi ya sa muka yanke shawarar rufe hanyar har sai an ɗauki mataki,” inji shi.

Muƙaddashin Daraktan Yaɗa Labaran Rundunar Soji ta 7 da ke Maiduguri, Laftanar-Kanar Ajemusu Y Jingina ya tabbatar da labarin da kuma tsare sojan da samun ya kashe direban motar.

“Rundunar runduna ta 7 ta Najeriya ta samu koke daga ƙungiyar NURTW reshen Jihar Borno cewa wani soja ya kashe wani direban babbar mota mai suna Mohammed Bello a wani shingen bincike a kan hanyar Dikwa-Gamboru a ranar 26 ga watan Disamba, 2023.

“Samun ƙorafin ke da wuya rundunarmu ta hanzarta ɗaukar mataki, kuma ƙoƙarin ganin iyalan mamacin sun samu adalci, an kama sojan da ake zargi, kuma an fara bincike kan lamarin.”

Ya bayyana cewa rundunar da ƙungiyar NURTW sun ƙulla yarjejeniya domin ganin an shawo kan lamarin cikin lumana, da kuma tabbatar da adalci ga iyalan mamacin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *