No menu items!

Sample Page Title

Date:

Yayin wasu mabanbantan samame da Jami’an Rundunar Vigilantin Jihar Kano suka gudanar, sunyi nasarar ƙwato wasu shanu da aka sace kimanin 60.

Alfijir labarai ta rawaito Kakakin ƙungiyar Kamalu Jibril Adam Sudawa ne, ya shaida hakan  a ranar Talata a birnin Kano.

Kamalu ya ce Jami’an Rundunar tasu sunyi Nasarar ƙwato Shanun ne a Ƙananan Hukumomin Rogo da Rimin gado yayin da aka kuma kama waɗanda ake zargin.

”Munyi nasarar kama shanu guda 60 , guda 18 daga ƙaramar hukumar Rogo kuma muka kama ɓarayi mutum biyu daga cikin su”.

” Mun ƙwato wasu shanun guda 42 kuma daga ƙaramar hukumar Rimin gado wanda nan kuma ɓarayi suka gudu”.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta ɗaure sojan Amurka na bogi a Kaduna

Kazalika kakakin ya ƙara da cewa rundunar tayi nasarar kama wasu ɓata gari a ƙwaryar birni wanda suke aikata laifuka.

Munyi nasarar kama wasu matasa guda biyu a ƙaramar hukumar Nasarawa wanda suka ƙware wajen sayar da kayan maye da kuma yiwa Mutane ta’addanci gami da yin Sojan gona da kayan Jami’an Vigilanti don bawa masu laifi mafaka”.

“Munyi nasarar gano waɗannan matasa ne ta hanyar bibiyar Lambar Jami’an mu wadda ake ƙira G.I.S ta hakan ne muka gano cewa ba jami’an mu bane”.

”Bayan kammala bincike da muka gudanar mun miƙa su hannun Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano domin girbe abinda suka shuka “.

Kwamandan Rundunar Vigilantin Alhaji Shehu Muhammad Rabi’u yayi ƙira da Al’umma su cigaba da bawa rundunar haɗin kai don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Jihar Kano.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...