No menu items!

Sample Page Title

Date:

Nyasha Chabika mai shekaru 24 da Flora Tofa mai shekaru 24, ‘yan madigo ‘yan ƙasar Zimbabwe da aka kama bayan wani kaset ɗin su na jima’i da aka kama, sun zargi ‘yan sanda da ƙwace tare da yin amfani da wayoyinsu.

‘Yan sandan Jamhuriyar Zimbabwe (ZRP) sun kama Nyasha da Flora a farkon Disamba 2023. Sun fuskanci tuhume-tuhume a gaban Kotun Majistare Masvingo Elizabeth Hanzie. Sai da Alkalin Kotun ta ba da belin su a kan dalar Amurka $100,000 kowannensu.

Da suke kukan cin mutuncin da ‘yan sanda suka yi musu, Nyasha da Flora sun zargi ‘yan sanda da mamaye sirrin su. Sun bayyana cewa ‘yan sandan sun umarce su da su miƙa wayoyinsu a wani ɓangare na binciken lamarin.  Rundunar ‘yan sandan ta kuma buƙaci da su ajiye kalmomin sirrin su.

KU KUMA KARANTA: Wata mata ta kashe mijin ƙawarta bayan ya kama su suna maɗigo a gadon sa

Sun kuma shaida wa alkalin kotun cewa jami’an ‘yan sandan suna yin fiye da bincike kawai. Masvingo Mirror  ya ruwaito cewa Nyasha da Flora sun yi iƙirari tare da zargin cewa jami’an ‘yan sanda a yanzu suna amfani da shafukansu na sada zumunta suna tura hotuna da bidiyonsu ga abokansu har da neman abokansu su basu kuɗi.

Har yanzu dai ana ci gaba da shari’ar su a halin yanzu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...