No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya rasu yana da shekaru 67 bayan fama da cutar sankarau

Alfijir labarai ta rawaito rahotanni sun bayyana cewa, Akeredolu wanda ya shafe kusan shekaru takwas yana gwamnan jihar Kudu maso Yamma ya rasu a wani asibitin Legas sakamakon kamuwa da cutar sankarar ɓargo.

A ranar 13 ga watan Disamba, gwamnan ya sake komawa hutun jinya. Bayanin hakan ya fito ne a wata sanarwa ɗauke da sa hannun babban sakataren yaɗa labaran sa, Richard Olatunde, inda ya jaddada ƙudirin gwamnan na ba da fifiko ga lafiyar sa da kuma samun cikakkiyar lafiya kafin ya ci gaba da aikinsa.

Yayin da Akeredolu ba ya nan, mataimakin gwamnan, Lucky Orimisan Aiyedatiwa, ya ɗauki nauyin gwamnan a matsayin muƙaddashinsa, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayyana.

Kafin tafiyar tasa na baya-bayan nan, gwamnan ya koma bakin aiki a watan Satumba, bayan ƙarin hutun jinya da ya yi a ƙasar waje wanda ya fara a watan Yuni.

KU KUMA KARANTA: Tsohon kakakin majilisar wakilai, Ghali Umar Na Abba, ya rasu

Sai dai rashin sanin halin lafiyarsa ya haifar da dambarwar siyasa yayin da yake ci gaba da gudanar da al’amuran jihar Ondo daga gidansa da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Tsare-tsare na nesa ya haifar da dagula dangantaka tsakanin magoya bayan Akeredolu da mataimakin gwamna Aiyedatiwa, wanda ya kai ga yunkurin tsige mataimakin gwamnan kafin da kuma bayan tafiyar Akeredolu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...