Tinubu ya ba da umarnin cafko waɗanda suka kashe mutane 115 a Filato

0
143

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su yi duk mai yiwuwa su cafko maharan da suka kashe mutane 115 a Jihar Filato.

A ranar jajibirin Kirsimeti ne ’yan bindiga suka kai farmaki a wasu yankuna sama da 15 a ƙananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi suka kashe sama da mutum 115.

Maharan na ranar Lahadi sun ƙone gidaje aƙalla 200, suka sace kayan abinci, suka lalata dukiya mai tarin yawa; Kawo yanzu dai babu wanda ya ɗauki alhakin hare-haren.

Tinubu ya yi tir da harin, sannan “ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta shiga yankin, su kuma kamo waɗanda suka yi ɗanyen aikin,“ in ji sanarwar da kakakinsa, Ajuri Ngelale ya fitar.

Sanarwar ta ce shugaban ya ba da umarnin tura kayan agaji yankin domin rage wa al’ummar raɗaɗin halin da suke ciki.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan ta’adda suna samun mafaka a makarantu a Barkin-Ladi tsawon shekaru — Gwamnan Filato

“Shugaba Tinubu ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Filato, tare da ba wa ’yan Najeriya tabbacin wa cewa waɗanda suka yi wannan aika-aika ba za su tsira ba,” in ji Ajuri.

Hare-haren da aka fara a Bokkos sun fantsama zuwa Barkin-Ladi, inda aka gano gawarwakin mutane 30, a cewar shugaban ƙaramar hukumar, Danjuma Dakil.

Gyang Bere, kakakin Gwamnan Caleb Mutfwang, ya ce “gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace don daƙile hare-haren da ake kai wa al’umma.”

Ƙungiyar kare hakkin bil Adama, Amnesty International ta soki gwamnati kan hare-haren.

“Hukumomin Najeriya sun kasa kawo ƙarshen munanan hare-hare a ƙauyukan Jihar Filato da wasu sassan Arewancin kasar,” in ji ƙungiyar a shafinta na X.

Arewa maso Yamma da Tsakiyar Najeriya sun daɗe suna fama da hare-haren ta’addancin ’yan bindiga musamman a kauyuka inda suke garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.

Leave a Reply