Sojoji sun kashe mahara 14, sun ceto mutum 14

Dakarun sojin Najeriya sun hallaka ’yan bindiga 14 a wani samame da suka kai a Jihohin Kaduna da Neja.

Sojojin sun kuma ceto mutum 14 da ’yan bindigar suka sace a yayin gudanar da aikin.

Muƙaddashin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar sojin, Laftanar-Kanar Musa Yahaya, ya ce a ranar Asabar sojojin suka kashe ’yan ta’adda biyu suka ƙwato bindigu guda biyu kirar AK-47 da babura a yankin Madawaki da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.

Sojojin sunceto wasu maza 13 da aka sace a ranar 13 ga Oktoba, 2023.

KU KUMA KARANTA: Yadda sojoji suka kashe Ali Kachalla da wasu 38, sun cafke 159

A Kaduna kuma, dakarun sun kashe ’yan ta’adda uku a yankin Madidaro da ke Ƙaramar Hukumar Birnin-Gwari sannan suka ƙwato bindiga AK-47 da wasu muggan makamai.

A Kidandan-Yadi da ke yankin Birnin-Gwari, kuma sun kashe ’yan ta’adda biyar tare da lalata sansaninsu sannan suka ƙwato babura 12.

Kazalika, dakarun sun ceto wani wanda aka yi garkuwa da shi a yankin Maro bayan fafatawa da maharan.

Yayin wani aiki da sojojin suka yi da safiyar Lahadi, sun yi wa ‘yan ta’addan Kwanar Batero da ke Kaduna kwanton ɓauna tare da kashe ɗaya daga cikinsu, sannan suka ƙwato makamai da alburusai yayin artabun.

A baya-bayan nan dai dakarun sojin Najeriya na ci gaba da kai wa ‘yan bindiga hari, inda suke ci gaba da kashe su tare da raunata da dama daga cikinsu.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *