No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta cafke wata mata mai bisa zargin sheƙa wa mijinta ruwan zafi saboda bai je biki da ita ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Litinin.

Hundeyin, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Disamba, inda aka kama wadda ake zargin bayan da rundunar ta samu labarin faruwar lamarin.

Ya ce an fara gudanar da bincike kan lamarin, kuma mijin matar na kwance a wani asibiti da ba a bayyana ba.

KU KUMA KARANTA: Mai gidan haya ta ƙona wadda take zaune a gidanta da ruwan zafi

Tun da farko wata majiya ta shaida wa NAN cewa matar ta fusata da mijin, wanda ya halarci ɗaurin auren abokinsa amma ya ƙi tafiya da ita.

NAN ta ruwaito cewa rikici ya ɓarke a tsakanin ma’auratan, lamarin da ya kai ga matar deɓo tafasasshen ruwan zafi ta kwara wa mijin nata.

Tun da fari ma’auratan sun shirya zuwa wurin bikin tare, amma daga baya mijin ya sauya shawarar tafiya shi kaɗai.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...