An amince da sabon kundin tsarin mulkin Chadi

0
130

Aƙalla kashi 86 cikin 100 na masu zaɓe a Chadi sun amince da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar wanda aka gudanar da ƙuri’ar raba gardama a kansa ranar 17 ga watan Disambar 2023.

‘Yan ƙasar Chadi sun amince da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar da kimanin kashi 86 cikin 100 a ƙuri’ar raba gardama da suka kaɗa a makon jiya, kamar yadda hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana a ranar Lahadi.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan adawa a ƙasar ke sukar zaɓen inda tuni wasu daga ciki suka ƙaurace wa ƙuri’ar.

Hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana cewa kashi 63.75 cikin 100 na masu zaɓe a ƙasar ne suka dangwala ƙuri’a, duk da ‘yan adawa sun ce adadin bai kai haka ba.

“Adadin da hukumomi suka sanar bai kai haka ba,” in ji Max Kemkoye, shugaban wata kungiya ta ‘yan adawa.

KU KUMA KARANTA: Sudan ta kori ma’aikatan jakadancin Chadi daga Khartoum

“A ranar zaɓe kowa ya ga cewa an ƙaurace wa kaɗa ƙuri’ar. “Sun yi maguɗi a zaɓen, inda suka rika ƙara tsawon lokaci da suka sanar a yau,” in ji Yoyana Banyara, shugaban ‘yan adawa na ƙasar wanda ya riƙa da’awar “ba a yi zaɓe ba”.

“Abin kunya ne ga ƙasar”. Sai dai a nasu ɓangaren, hukumomin sun ce baya ga wasu “ƙananan matsalolin da aka samu”, an gudanar da zaɓen raba-gardamar lafiya.

Sakamakon zaɓen a halin yanzu na wucin-gadi ne inda ake sa ran Kotun Ƙoli za ta tabbatar ko kin tabbatar da zaɓen a ranar 28 ga watan Disamba.

Ƙuri’ar raba gardamar da aka gudanar wani muhimmin mataki ne na mayar da mulki ga farar hula kafin ƙarshen shekarar 2024, kamar yadda shugabannin sojin ƙasar suka yi alƙawari.

Sai dai shugabannin ‘yan adawa da dama sun bayyana cewa wannan wata hanya ce ta sharar fage ce ga shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Mahamat Idriss Deby Itno domin zama shugaban ƙasar.

Leave a Reply