Abokinsa da matarsa su suka shirya komai – Sanusi Ɗahiru Gwarando

0
165

Ɗan uwana ne na jini kuma ƙani yake a gare ni. Ya gamu da ajalin sa ne a jihar Kano ƙaramar hukumar Tarauni cikin unguwa uku.

Abokin sa da matar abokin nasa, su suka shirya komai da kan su, kuma matar ta amsa yi masa kisan gilla..!

Matar ta amsa da bakin ta ita ta caccakka masa wuƙa a wuya da kahon zuciya da kuma gefen cikin sa har ya mutu..!

Yanzu haka mutum uku suna hannun jami’an tsaro mijin da matar da kuma wanda ya tattare shi ya sa lifafa da sunan ya masa wanka

Hoton yana da daga hankali.
Allah ya kare mu daga miyagun mutane, masu hasada da shariin aikata mumunar abu

ME MIJI DA MATAN NAN SUKE ƘOƘARIN ƁOYEWA..?

Hoton marigayi Nafiu da mahaifin sa da kuma miji da matar da ake tuhuma da kisan sa a wani asibiti lokacin da yake jinya, yan makwanni kafin kashe shi…!!!

TAKAITACCEN TARIHIN MARIGAYI NAFI’U

An haifi Nafiu a ranar Alhamis 17 ga watan 3 shekerar 1988, a unguwar Rariya ƙaramar hukumar Bauchi jihar Bauchi, sunan mahaifin sa Alh Hafizu Salihu Gorondo ɗan Asalin jihar Bauchi karamar hukumar Ganjuwa garin Gorondo gundumar Zarah.

ME YA KAI NAFI’U JIHAR KANO..?

Kafin harkar kasuwanci Alh Nafi’u, ya samu kan sa a jerin matasan da suke sha’awan karatu kuma wannan shine dalili na farko da ya kai shi jihar har ya samu kai wa ga matakin Diploma.

MENENE ALAƘAR NAFI’U DA ALH DAYYIBU?

Abokin sa ne da suka fara abota tun a makaranta kamar yadda ya shaida wa mahaifin sa tun lokacin fara alaƙar su, kuma ya shaida wa mahaifin sa cewar Alh Ɗayyibu abokin sa ne kuma mai gidan sa da suke harkan kasuwanci a kantin kwari.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sandan jihar Kano sun kama matar da ake zargi da kashe wani mutum (Bidiyo)

Kuma alaƙar ɗana da Alh Dayyibu takai matakin da har ƙaramin ɗan su suka turo tun daga jihar Kano zuwa Bauchi na yi ɗawainiyar yaye shi, na mayar da shi gidan su a Kano.

MENENE YA KAI NAFI’U GIDAN ALH DAYYIBU HAR AKA KASHE SHI A GIDAN?

Kafin rashin lafiyan da ya kwantar da Nafiu a asibitin EXPERT ALINCE dake jihar Kano (wanda aka masa aiki kuma ya warware har aka sallame shi), Nafi’u na zaunane a gidan haya shi kaɗai, kuma dalilin rashin lafiyar ne yasa ya koma gidan mai gidan sa kuma abokin sa da zama, kamar yadda mahaifin sa ya shaida.

KO A KWAI WATA MATSLA TSAKANIN NAFI’U DA ALH DAYYIBU DA YA KAI SU GA WANNAN HALI?

Mutum ukun nan su kaɗai za su iya faɗin hakikan abinda yake tsakanin su Ɗayyibu da matar sa sai kuma Nafiu, sai dai kuma Nafi’u baya raye balle aji ta bakin sa.

Amma ana sa jawabi mahaifin Nafi’u yace ɗan sa ya taɓa gaya masa cewa yana bin aminin sa bashi, kuma kuɗaɗen suna da ɗan yawa, amma ban sani ba ko wannan shine dalilin saɓanin su da ya kai ga wannan mataki.

Daga ɓangaren shi Alh Dayyibu kuma har yanzu hukumar yan sanda ta jihar Kano tana ci gaba da tsare shi tare da binciken sa kuma har yanzu ba ta fitar da sakamakon binciken ta ba kan abinda ya faru tsakanin su.

Sai dai kuma bayanai sun tabbatar a gidan shi Alh Dayyibu aka yi kisan kuma a na tuhumar sa da yunƙurin ɓoye hakikanin abinda ya faru.

ME YASA KUMA DAME AKE TUHUMAR ALH DAYYIBU DA MATAR SA HAFSA KAN KISAN GILLA GA NAFI’U?

Daga jawabin Alh Dayyibu ana tuhumar sa ne sabo da shi da kan sa ya ƙira mahaifin Nafiu ya shaida masa mutuwar ɗan sa Nafi’u amma da sigar cewar jinyar sa ta farko itace sanadin mutuwar sa.

Kuma ya ɓoye batun cewa kashe shi aka yi, ya yi saurin neman agajin wani mutum suka lulluɓe Nafi’u a Zannuwa da yadi duk da sunan an masa wanka saura sallan Janaiza kawai, kuma wannan mutum ya amsa cewa Alh Dayyibu shi ya gayyace shi wannan aiki.

SHIN MEYE KE TSAKANIN NAFI’U DA MATAR ALH DAYYIBU HAR AKA TUHUMETA A MATSAYIN MUTUM NA FARKO DA AKE ZARGI DA AIKATA KISAN?

Wannan shine lamarin da yafi komai ɗaure kai, sai dai a karon farko ita da kanta gaban ‘yan sanda na wannan unguwa ta amsa cewar itace ta yi wannan aika aika, kamar yadda mahaifin Nafi’u ya shaida.

Kuma har yanzu a bayanan da ake samu wannan batu a kan sa take, sai dai dalilan aikata wannan ɗanyen aikin ne ta gaza gamsar da masu tambaya, hakan ne yasa ake ci gaba da tsare ta da kuma tambayar ta hakikanin dalilin da suke boyewa.

ABIN ƊAURE KAI CIKIN WANNAN LAMARI NA KISAN GILLA!

Ga duk wanda ya yi ido biyu da hakikanin hotonuna masu tada hankali na gawan Alh Nafiu Hafeez Gorondo, zai shiga shakku da kokwanto na kai tsaye kuma zuciyar sa zata ta nanata tambaya kan yadda za’a ce mace ɗaya kuma ƙarama kamar Hafsa zata iya aikata wannan ɗanyen aiki ga tsayayyen da na miji kamar Nafiu ba tare da gudunmawar kowa ba.

Abin jira a gani dai shine, sakamakon binciken ƙarshe da hukumar yan sanda ta jihar Kano zata fitar da kuma irin, hukuncin da kotu zata yanke kan wannan al’amari.

Leave a Reply