No menu items!

Sample Page Title

Date:

A ƙoƙarinta na kare rayuka da dukiyoyi Gombe, Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) ta girke jami’ai 780 domin sintiri a Jihar Gombe a lokacin bukukuwan kirsimeti da sabuwar Shekara.

Kwamandan hukumar a jihar, Muhammad Bello Mu’azu, ne ya sanar da hakan, yana mai umurtar Kwamandojin Yankin da na ƙananan hukumomi da sauransu cewa su tabbatar sun tura isassun jami’ai a lungu da sakon jihar.

A cewar sanarwar, za a tura jami’an ne a wuraren ibada da kasuwanni da tashohin mota da kuma wuraren shakatawa.

Sannan sai ya buƙaci jama’a da su yi bukukuwan a tsanake wajen kiyaye doka da oda domin jami’ansa za su yi aikinsu ba sani, ba sabo.

A cewarsa, za su tabbatar da ganin sun tsare rayuka da dukiyoyi yadda ya dace kafin lokacin kirsimeti da kuma Sabuwar Shekara.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...