An gurfanar da wani matashi a kotu a Kano bisa zargin kashe abokinsa saboda naurar sauraren sauti ta Bluetooth.
Ana zargin matashin ya caka wa abokin nasa mai suna Abdulazeez Aliyu, wuƙa a ciki ne, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Takardar ƙarar ta bayyana cewa tun da farko wata sa-in-sa ce ta shiga tsakanin abokan biyu a kan abin saurare na wayar hannu (Bluetooth).
Sai dai wanda ake zargin ya musanta laifin da ake tuhumar sa da aikatawa na kisa wanda, ya saɓa da sashe na 221 a Ƙundin sharia na Pinal Kod.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Binta Ibrahim Galadanchi, ta Kotun Majistare Mai Lamba 19 da ke zamanta a Nomanslan ta bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan yari.
Daga nan ta ɗage sauraren shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Janairu, 2024.