No menu items!

Sample Page Title

Date:

An gurfanar da wasu maza su biyar kan zargin su da yin taron dangi wajen kashe wata mata saboda mafarkin da wata ta ba su labari a Jihar Kano.

Kotun Jihar Kano mai lamba 14 da ke zamanta a titin Miller ta gurfanar da su ne kan zargin haɗa baki da kishe matar saboda zargin ta da maita.

Mai gabatar da ƙara, lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Sorondinki ya shaida wa kotun cewa waɗanda ake zargin su biyar suka haɗu suka kashe wata mata mai suna Dahara Abubakar.

Barista Lamido Abba Sorondinki ya ce a garin Dadin kowa da ke ƙaramar hukumar Wudil sakamakon ne wata mata mara lafiya da ta bayyana cewa ta yi mafarki cewa marigayiyar ta biyo ta da wuka.

Hakan ya sa waɗanda aka gurfanar suka dogara da mafarkin nata har suka yi wa marigayiya Malama Dahara Abubakar wannan ɗanyen aikin.

KU KUMA KARANTA: Ya kashe kawunsa kan zargin maita a Adamawa

Dukkanin waɗanda ake zargin sun musanta laifukan da ake zargin su na haɗin baki wajen aikata kisa da suka saɓa da sashe na 97 da 221 na Kundin Pinal Kod.

Alkalin Kotun Mai Shari’a Zuwaira Yusuf ta aike da waɗanda ake zargi gidan yari ta kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Janairu 2024.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...