Sabon Sarkin Kuwait ya caccaki gwamnati a wurin rantsar da shi

0
157

Sheikh Meshal al-Ahmad al-Sabah, ya karɓi rantsuwar fara aiki a matsayin sabon Sarkin ƙasar Kuwait.

A jawabinsa na karɓar rantsuwa, Sheikh Meshal, ya soki ɓangaren zartarwa da na majalisar dokokin ƙasar da ctuar da kasar da kuma al’ummarta.

Sheikh Meshal ya zargi mahukutan ƙasar da “naɗa mutane a mukamai ba bisa adalci ba, kuma saɓanin abin da dokar ƙasar a tanada.”

Ya yi wannan caccaka ne a zauren majalisar da aka rantsar da shi a safiyar Laraba.

Ya kuma nuna rashin amincewarsa da afuwar gwamnatin ƙasar ta yi wa wasu fursunoni da ’yan adawa da kuma abin da ya kira lalacewar al’adun Kuwait.

A cewarsa, “ya zama dole mu yi karatun halin da muke ciki, musamman a ɓangaren tsaro da tattalin arziki da kuma yanayin rayuwarmu”.

KU KUMA KARANTA: Sarkin Kuwait Nawaf Al-Ahmad Al-Sabah ya rasu

“Yana muhimmanci mu ƙara waiwaye da bibiya da kuma tabbatar da gaskiya bisa tsarin dokar ƙasa wajen yin gyara kan yadda ake watsi da rayuwar al’ummar kasa.”

Sheikh Meshal, mai shekaru 83, ya kasance mai gudanar da ƙasar Kuwait na yau da kullum a zamanin mulkin ɗan uwansa Sheikh Nawaf, saboda rashin lafiyarsa.

Sheikh Nawaf ya rasu a ranar Asabar.

Leave a Reply