Miji ya kashe matarsa saboda taliyar yara

0
145

Wani magidanci ya hallaka matarsa saboda taliyar yara a yankin Olota da ke ƙaramar hukumar Alimosho a Jihar Legas.

Ana zargin magidancin ya yi wannan aika-aika ne bayan da ya dawo daga aiki ya samu matarsa ta dafa taliyar yara maimakon abincin da ya fi so.

Wata majiya da ta buƙaci a sakaya sunanta saboda tsaro, ta ce mijin ya bar matar kwance bayan ya doke ta da dutse a kanta.

Majiyar ta ce wani makwabcin magidancin ne ya ƙira magidancin ya sanar da shi matarsa na cikin wani yanayi.

Makabtan ne suka garzaya da matar zuwa asibiti inda a can ne aka tabbatar da rasuwarta.

KU KUMA KARANTA: Wani matashi ya kashe mahaifiyarsa

Shaidu sun ce ’yan sanda sun cafke miji inda suna gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru a tsakaninsa da matarsa.

Amma rundunar ’yan sandan jihar Legas ta ce kawo yanzu ba a tabbatar da cewar mijin ne ya kashe matar ba.

Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin ya ce suna kan bincike kuma da zarar sun kammala za su bayyana wa jama’a sakamakon binciken da suka samu.

Leave a Reply