Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christoper Musa ya ce rundunar tsaro za ta hukunta duk wanda ta samu da hannu a harin da jirgin soji a ƙauyen Tudun Biri a Jihar Kaduna.
Janar Musa ya sanar a ranar Juma’a cewa da zarar rundunar ta kammala bincike kan harin, duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.
Ya shaida wa manema labarai a Hedikwatar tsaro da ke Abuja cewa babu yadda za a zura ido wani ya yi irin wannan aika-aika ba tare da an hukuna shi ba.
KU KUMA KARANTA: Sanatoci sun sallama albashinsu na Disamba ga nutanen Tudun Biri
A cewarsa, “a aikin soja ba ma kare masu laifi, saboda haka za mu yi komai a fili, babu rufa-rufa.
“Mun sha hukunta dakarunmu da ke rundunar Operation Hadin Kai, wasunsu kuma soji ta yanke musu hukuncin dauri a kurkuku.”