No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wasu ’yan bindiga sun hallaka hakimin garin Sarkin Kudu da ke ƙaramar hukumar Ibbi a Jihar Taraba.

Wata majiya a yankin ta shaida wa wakilin Aminiya cewa ’yan bindigan sun afka fadar hakimin mai suna Ali Hakimi da misalin karfe 12.30 na daren jiya.

Majiyar ta ce ’yan bindigan sun tilasta wa hikimin fitowa daga ɗakinsa zuwa kofar fadarsa ta hanyar nuna masa bakin bindiga.

A kofar fadar hakimin ne ’yan bindigan suka harbe shi har lahira sannan suka tsere, har yanzu ba a gano su ba.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindiga bakwai a Kaduna

Ali hakimi ƙani ne ga sarkin masarautar Sarkin Kudu, ɗaya daga cikin masarautun da tsohon gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku ya ƙirƙiro a lokacin mulkinsa.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi ya ci tura, domin wayarsa a kashe a lokacin da wakilin, mu ya ƙirashi dangane da labarin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...