Gwamnan Anambra na farko, Chukwuemeka Ezeife, ya rasu

Gwamnan Jihar Anambra na farko, Dokta Chukwuemeka Ezeife ya riga mu gidan gaskiya.

Dokta Chukwuemeka Ezeife, wanda jigo ne a ƙungiyar kabilar Igbo ta Ohaneze Ndigbo, ta rasu ne a sakamakon rashin lafiya a daren Alhamis.

Ya rasu ne a Babban Asibitin Tarayya da ke Abuja, kamar yadda Cif Rob Nawkairea Ezeife ya sanar a madadin iyalan mamacin.

“Muna sanar da rasuwar ɗanmu, Chukwuemeka Ezeife, CON, tsohon Babban Sakatare kuma gwamnan jihar Anambra na farko”

Chukwuemeka Ezeife tsohon mashawarcin shugaban ƙasa ne, kuma tsohon mai neman takarar shugaban ƙasa.

“Nan gaba za mu sanar da tsare-tsaren jana’izar,” in ji sanarwar rasuwar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *