Isra’ila ta ce za ta ci gaba da yaƙi da Hamas ko babu goyon bayan wata ƙasa

0
132

Sanarwar tasa na zuwa ne bayan da shugaban Amurka Joe Biden ya caccaki yadda Isra’ila ke ci gaba da luguden wuta ba kakkautawa a kan Zirin Gaza, a matsayin martani ga harin ranar 7 ga watan Oktoba  da Hamas ta kai mata.

A ranar laraba ƙawayen Isra’ila sun zafafa matsin lamba a kanta sakamakon wannan yaƙin da ta ke yi da Hamas, inda ma Amurka da kanta ta bayyana hare-haren a matsayin na kan mai-uwa-da-wabi.

Ko a ranar talata sai da babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da wani kudiri na neman tsagaita wuta, lamarin da ya ta’azzara matsin lamba a kan Isra’ila da Amurka.

KU KUMA KARANTA: Jakadiyar Isra’ila a Birtaniya ta ƙi amincewa da samar da ƙasashe biyu a matsayin mafita ga yakin Gaza

Ya zuwa yanzu adadin waɗanda suka mutu a wannan hare-haren da Isra’ila ke kai wa Zirin Gaza tun bayan harin 7 ga watan Oktoba ya zarce dubu 18, kuma har yanzu tana ci gaba da hare-hare, duk da buƙatar Amurka ta sara ana duban bakin gatari.

Mahukuntan yankin Falasɗinu sun ce samamen da Isra’ila ta fara a garin Jenin tun a ranar Talata da ta gabata ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa 10.

Leave a Reply