Tinubu ya sallami shugabannin hukumomin sufurin jiragen sama

0
142

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami shugabannin hukumomi shida da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama.

Hadimin Shugaban Ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ta sanar a daren karaba cewa tinubu ta sallami shugabannin hukumomin ne domin ingantar harkar sufurin jiragen saman Najeria da kuma share hawayen matafiya.

Waɗanda aka sallama sun haɗa da Shguaban Hukurmar Kula filaen jirgin sama (FAAN), Kabir Yusuf Mohammed da Shugaban Hukumar Sufurin Jiragen Sama (NCAA) Kafin Shuaibu Nuhu, da kuma Shugaban Kwalejin Koon ukun Jirgin Sama (NCA) Kafin Alkali Mahmud Modibbo.

KU KUMA KARANTA: Akpabio ya buƙaci Tinubu ya hana ministoci tafiya ƙasashen ƙetare

Suran sune Shugaban Hukumar Kula da Sarafin Samaniya (NAMA), Tayib Adetunji Odunowo; Shugaban Hukumar Binciken Sufurin Jirage (NSIB), Akinola Olateru; da Shugaban Hukumar Hasashen Yanayi, Farfesa Mansur Bako Matazu.

Ajuri ya ƙara da cewa Tinubu ya naɗa sabbin shugabannin hukumomin kamar haka;

Sabuwar Manajana-Darkatan FAAN ita ce, Olubunmi Oluwaseun Kuku, sai Injiniya Umar Ahmed Farouk a matsayin sabon Manajan-Daraktan NAMA a yayin da Alex Badeh Jr. ya zama sabon Manajan-Darakan NSIB.

Farfesa Charles Anosike zai jagoranci NIMET, Kyaftin Chris Najomo zai jagoranci NCAA sai Josetp Shaka Imalighwe kuma NCAT  a matsayin mukaddasin shugaba.

Tinubu ya kuma ba wa ministan ma’aikatar, Festus Keyamo izinin kammala aikin ɗaukar shugaban jami’ar tuƙin jiragen sama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here