Masar za ta ƙara yawan fetur ɗin da ake shigarwa Gaza a kullum

0
170

Masar ta sanar a jiya Laraba cewa, za ta ƙara yawan man da ake aika wa a kullum zuwa Zirin Gaza daga lita 129,000 zuwa lita 189,000 bisa yarjejeniya da Isra’ila.

Shugaban hukumar yaɗa labaran ƙasar Masar Diaa Rashwan ya bayyana cewa Masar na ci gaba da kokarin tabbatar da shigar da kayayyakin jinƙai zuwa Zirin Gaza.

Ya ƙara da cewa, tun a ranar Talatar da ta gabata ne, motocin agaji suka fara tsallakawa ta iyakar Rafah zuwa mashigar Karem Abu Salem domin aiwatar da yarjejeniya da ɓangaren Isra’ila.

Ana sa ran hakan zai saukaka isar manyan motocin dakon kaya zuwa Zirin Gaza, tare da ƙara adadinsu zuwa 60 zuwa 80 a kullum.

KU KUMA KARANTA: Jakadiyar Isra’ila a Birtaniya ta ƙi amincewa da samar da ƙasashe biyu a matsayin mafita ga yakin Gaza

Rashwan ya lura cewa adadin manyan motocin da suka tsallaka daga kan iyakar Rafah zuwa Zirin Gaza ya kai 4,057 tun lokacin da aka fara shigar da kayan agaji cikin yankin daga ɓangaren Masar na mashigar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here