Jakadiyar Isra’ila a Birtaniya ta ƙi amincewa da samar da ƙasashe biyu a matsayin mafita ga yakin Gaza

0
150

Jakadiyar Isra’ila a Birtaniya ta yi watsi da yiwuwar samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu a matsayin hanyar warware rikicin da ya biyo bayan mamayar da Isra’ila ta yi wa yankunan Falasɗinawa na tsawon shekaru, a wata hira da ta yi da gidan talabijin na Sky News.

“Ina ganin lokaci ya yi da duniya za ta fahimci tsarin Oslo ya gaza a ranar 7 ga watan Oktoba, kuma muna buƙatar sake gina wani sabon tsari,” in ji Tzipi Hotovely, yayin da take magana kan ranar da ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa ta Hamas ta ƙaddamar da wani harin ba-zata a Isra’ila.

Ta ƙara da cewa “Isra’ila ta sani a yau kuma ya kamata duniya ta sani cewa yarjejeniyar Oslo ta gaza saboda Falasɗinawa ba su taɓa son samun ƙasa kusa da Isra’ila ba, suna son samun ƙasa tun daga kogi har zuwa teku.”

KU KUMA KARANTA: An kai wa jirgin ruwa hari a Bahar Maliya yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza

Hotovely ta tambayi ɗan jaridar Mark Austin, dalilin da ya sa ya damu da batun tsarin samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu, bayan da ya tambaye ta ko wannan yunƙurin ya mutu ne.

Da aka tambayi ra’ayinta game da kalaman shugaban Amurka Joe Biden na cewa Isra’ila tana “rasa goyon baya” kan harin bama-bamai da take kaiwa Gaza, sai ta ce “Amurkawa suna yaƙar ISIS [Daesh] a Mosul, [Iraƙi], akwai mutanen da aka kashe a Mosul daidai ko fiye da na Gaza.”

Hotovely ta yi iƙirarin ƙarya cewa Isra’ila “tana yin duk abin da zai hana asarar rayuka” kuma ta ce makarantun Majalisar Ɗinkin Duniya a Gaza “sun zama makarantun ta’addanci.”

Leave a Reply