No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani matashi mai suna da Sadiq Idrissu, ya kashe mahaifiyarsa a Jihar Adamawa, kuma ya bayyana cewa bai yi nadamar kisan gillar da ya yi mata ba.

Alfijir labarai ta rawaito matashin mai shekaru 30, ya kashe mahaifiyarsa ne ranar 05 ga watan Disemba 2023, a garin Boga cikin ƙaramar hukumar Gombi a jihar, maimakon nadama kan kisan gillar da yai mata, amma cewa “ban yi nadamar kisan da na yi wa mahaifiyata ba” in ji matashin.

KU KUMA KARANTA: Ɗan kasuwa ya nemi kashe matarsa don ya ƙara jari a shagonsa

Ya ci gaba da cewa “na kashe ta ne, saboda ta bayyana min ita mayya ce, da ma jama’a na zarginta da maita, kuma gaskiya ne, domin tana aikata wasu abubuwan mamaki, musamman da daddare.

“Mamana tana bayyana min a cikin mafarki a matsayin mayya, tana kuma jefa min tsoron da ke hana ni yin bacci da daddare” in ji matashin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...