EFCC ta gurfanar da mata da miji a kotu kan zargin zambar naira miliyan 410

0
134

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa EFCC ta gurfanar da wasu mata da miji a gaban kotu inda aka tuhumarsu bisa kan laifuka biyar da suka haɗa da zargin karkatar da kuɗaɗe har N410,518,000.

An gurfanar da ma’auratan Aisha Salihu Malkohi da aka fi sani da Ummitah Arab Money da mijinta Abubakar Abubakar Sadiq Mahmoud ne a gaban wata babbar kotu a jihar Kano ranar Juma’ar da ta gabata.

Ana zargin su da karɓar kuɗi har naira 225,259,000 na wata Farida Ibrahim daga watan Janairu har zuwan Disamban 2022 da nufin za su sayo mata motoci 64 daga Saudiyya, kamar yadda sanarwar da EFCC ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin ta faɗa.

“Kun karɓi kuɗaɗen duk da cewa kun san ƙarya ne, don haka kun aikata laifi a ƙarƙashin dokar laifukan da suka shafi zamba ta 2006,” kamar yadda takardar tuhumar ta ce.

Wacce ake zargin dai ta amsa dukkan laifuka biyar ɗin da aka karanta mata, inda nan da nan lauyan EFCC Zarami Mohammed ya nemi kotu da ta sanya ranar yanke hukunci.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta fitar da matakai takwas na kare kai daga masu damfara da katin ATM

Sai dai lauyan ma’auratan ya nemi a ba da belinsu amma hakan bai samu ba.

Kotu ta bai wa EFCC izinin ci gaba da riƙe su har sai zama na gaba da za a yi ranar 15 ga watan Disamban 2023.

EFCC ta kama Aisha ne bayan da wasu mutum biyu Farida Ibrahim da Ibrahim Mohammed Abdulrahman suka shigar da ƙorafi a gabanta suna zargin Aisha da haɗa baki da mijinta wajen zambatar su, da nufin za su sayo musu motoci da gwala-gwaldai da kayan lantarki da kayan kicin daga Saudiyya.

“Karɓar korafin ke da wuya sai hukumar EFCC ta ƙaddamar da bincike wanda ya gano cewa Aisha ta karɓi kuɗi har naira miliyan ɗari huɗu da goma da dubu ɗari biyar da goma sha takwas, N410,518,000 ta asusun bankunan kamfaninta, Golden Grass Hill International Ltd da asusun mijinta na banki.

Kazalika binciken EFCC ya gano cewa Aisha da mijinta Abubakar (wanda har yanzu bai zo hannu ba), sun karkatar da kuɗaɗen zuwa asusun bankuna daban-daban.

Leave a Reply