An kai wa jirgin ruwa hari a Bahar Maliya yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza

0
126

Wasu cibiyoyin leken asiri masu zaman kansu sun ce an kai wa wani jirgin ruwa hari a gabar tekun Yemen na Bahar Maliya.

Harin da aka kai kan jirgin ruwan ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan tawayen Houthi na Yemen ke ci gaba da yin barazana a kan safarar jiragen ruwa na kasuwanci a yankin saboda yaƙin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza.

‘Yan Houthi dai ba su ɗauki alhakin kai harin ba, ko da yake kakakin rundunar ‘yan tawayen Birgediya Janar Yahya Saree ya ce wata muhimmiyar sanarwa za ta fito daga gare su nan da sa’o’i masu zuwa.

Cibiyoyin leƙen asiri masu zaman kansu Ambrey da Dryad Global sun tabbatar da cewa harin ya afku ne a kusa da mashigin Bab al-Mandeb da ke raba gabashin Afirka da yankin Larabawa, amma sun ce ba su da wani ƙarin bayani.

Wani makami mai linzami da aka harba daga yankin ƙasar Yemen da ke ƙarƙashin ikon Houthi ya kai hari kan wani jirgin ruwan dakon kaya na kasuwanci, inda ya yi sanadin tashin wuta da jawo ɓarna, kamar yadda jami’an tsaron Amurka biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Wani jami’in ya ce harin da aka kai kan jirgin ruwan na STRINDA ya faru ne daga tazarar kilomita 60 a arewacin gabar tekun Bab al Mandab.

Jami’an sun ce jirgin ruwan Amurka na agaji na Mason ya je wurin kuma yana bayar da agaji. Ba a dai fayyace ko STRINDA na da wata alaƙa da Isra’ila ko kuma yana kan hanyar zuwa tashar jiragen ruwa ta Isra’ila ba ne.

Leave a Reply