Mutane da dama ne suka mutu yayin da wasu suka jikkata sakamakon wani harin bam da Isra’ila ta kai a unguwar Shujaiya da ke birnin Gaza a cewar kafar yaɗa labaran Falasɗinu.
Kamfanin dillancin labaran Falasɗinu Wafa, ya bayar da rahoton cewa, an ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a wasu yankuna da dama a Gaza.
Hukumar ta ce, Isra’ila ta fi kai hare-haren a yankunan gabashin Khan Younis da kuma gabar tekun Rafah da ke kudancin Gaza, yayin da jiragen yakin Isra’ila suka fi kai hari a tsakiyar Gaza.
A ranar 1 ga watan Disamba ne Isra’ila ta sake kai farmakin soji a Zirin Gaza bayan kawo ƙarshen tsagaita wuta na tsawon mako guda da kungiyar Hamas ta Falasɗinu.
Aƙalla Falasɗinawa 17,177 aka kashe yayin da wasu fiye da 46,000 suka jikkata sakamakon hare-haren wuce gona da iri da aka kai a yankin tun ranar 7 ga watan Oktoba bayan harin ba-zata da ƙungiyar Hamas ta kai.