MƊD ta nemi Najeriya ta biya diyyar mutanen da jirgin soji ya kashe

0
118

Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ta buƙaci gwamnatin Najeriya ta biya diyya ga duk mutanen da jiragen soji suka kai wa hari a ƙasar.

MƊD ta kuma yi tir da harin bom da sojojin Najeriya suka kai da jirgi mara matuki kan taron Mauludi a yankin Tudun Biri a Jihar Kaduna bisa kuskure.

Majalisar ta ƙara da cewa harin na daren Lahadi da aka kashe fararen hula aƙalla 85 ba shi ne farau ba, don haka dole gwamnati da sojojin ƙasar su ɗauki matakin hana sake faruwar hakan.

“Muna ƙira ga gwamnatin Najeriya ta yi zuzzurfan bincike kan karya dokar ƙasashen duniya da aka yi wajen kashe fararen hula tare da kuma raunata da a harin jirgin sojin.

“Sannan gwamnati ta ba da diyya da cikakkiyar kulawa ga duk mutanen da jiragen soji suka kai wa irin waɗannan hare-hare.

“Dole ne kuma rundunar tsaron Najeriya ta yi nazari tare da inganta dokoki da tsarin aikinsu domin kauce wa irin haka,” a cewar kakakin MƊD, Seif Magango a ranar Larba.

Rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta ɗauki alhakin harin, wanda ta ce jirgin ta ya yi kuskuren jefa bom kan fararen hula a lokacin da take fatattakar ’yan ta’adda a yankin ƙaramar hukumar Igabi.

KU KUMA KARANTA: Zanga-zanga ta ɓarke a majalisa kan harin Mauludin Kaduna

Rundunar sojin ta bayyana cewa ibtila’in ya faru ne bayan da ta yi kuskuren fassara motsin fararen hular da ke halartar taron Mauludin a matsayin ’yan ta’adda, har ta jefa musu bama-bamai.

Amma Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce, “Mun kaɗu da abin da sojojin suka faɗa cewa sun yi kuskuren fassara motsin fararen hular … wani babban abin damuwa shi ne harin ya saba wa dokokin ƙasashen duniya.”

Igabi na cikin yankunan jihar Kaduna da suka ’yan ta’adda da fi addaba, inda suke yin kisan gilla suna ƙona dukiyoyi ko sacewa, tare da garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa.

Leave a Reply