Hukumar FAAN ta hana tafiya da jakar ‘Ghana Must Go’ a filayen jirgin sama

Hukumar Kula da filayen Jiragen sama ta Ƙasa (FAAN) ta haramta amfani da jakar tafiye-tafiye da aka fi sani da Ghana Must Go ga matafiya masu amfani da filayen jiragen saman ƙasar.

Alfijir labarai ta rawaito cewa, dokar ta shafi masu tafiya ta filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa.

FAAN ta ce amfani da jakar Ghana Must Go a matsayin harkar tafiye-tafiye na jawo manyan kamfanonin jiragen sama asara tare da lalata na’urar ɗaukar kaya.

FAAN ta bayyana hakan ne a wata sanarwa mai taken, ‘ Hana Amfani da Ghana Must Go’ mai ɗauke da sa hannun Manaja, Ma’aikatar Jiragen Sama, Henok Gizachew da kwanan wata 24 ga Nuwamba.

KU KUMA KARANTA: Jirgin saman ‘United Nigeria Airlines’ ɗauke da fasinjoji 50 ya tsallake rijiya da baya

An ba da sanarwar ne ga kamfanonin jiragen sama masu amfani da filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa yayin da kamfanonin jiragen suka sanar da abokan hulɗarsu da fasinjoji.

Ɗaya daga cikin kamfanonin jirgin a cikin wani sako ga fasinjojin ya ce, “Ana sanar da mu cewa daga ranar 25 ga Nuwamba, 2023, an haramta amfani da Ghana Must Go’ don tafiya a cikin jirginmu.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *