‘Yan sanda da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaron Najeriya sun kashe ‘yan bindiga sama da hamsin a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin ƙasar, in ji rundunar ‘yan sandan ƙasar.
Lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Bali ranar Talata, ko da yake rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana haka ne ranar Alhamis da maraice, kamar yadda kakakinta Abdullahi Usman ya shaida wa gidan talbijin na Channels Television.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaron sun kai samame ne bayan sun samu korafi daga mazauna yankin cewa ‘yan bindigar sun addabe su, abin da ya sa jami’an tsaro suka yi musu kwanton-ɓauna inda suka kashe fiye da hamsin.
“Rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba ta samu bayanai cewa ɗaruruwan ‘yan bindiga da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun kai hari kauyen Tonti a yankin Maihula na ƙaramar hukumar Bali.
KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindiga bakwai a Kaduna
‘Yan bindigar sun kai hari ne da asuba yayin da mutane suke sallar asubahi, inda suka rika yin harbi kan mai-uwa-da-wabi,” a cewar Abdullahi Usman.
A wannan lokaci ne jami’an tsaro suka far musu da harbe-harbe inda suka kakkashe su yayin da wasu suka samu munanan raunuka. Daga bisani bincike ya nuna cewa an kashe ‘yan bindiga sama da hamsin, in ji kakakin rundunar ta ‘yan sanda.
Sai dai ya ce ‘yan bindigar sun kashe mutum goma sha biyu kafin isar jami’an tsaro, yana mai cewa yanzu haka jami’ansu sun bazama domin kamo sauran ‘yan bindigar da suka tsere dauke da raunukan bindiga.
Jihar Taraba ta daɗe tana fama da rashin tsaro sakamakon rikicin ƙabilanci, ko da yake ba a cika samun rahotannin hare-haren masu garkuwa da mutane ba.
Jami’an tsaron ƙasar sun ce suna ƙara ƙaimi wurin daƙile rashin tsaron da ya addabi yankin, wanda ya yi sanadin ɗaruruwan jama’a a shekarun baya-bayan nan.