EU ta dakatar da shirin sanya idanu a zaɓen Jamhuriyar Congo

0
181

Ƙungiyar Tarayyar Turai, ta ce ta soke shirinta na sanya idanu kan zaɓen Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo, sakamakon wasu dalilai masu cike da sarkakiya da ta yi nazari a kai.

Kakakin ƙungiyar, Nabila Massrali, ta ce tawagar masu sanya idanu da aka tura Jamhuriyar Congo, an gaza tura su sassan ƙasar, sakamakon matsalolin tsaro.

Ta ce hanyoyin sadarwar salula na cike da ƙalubale ga masu aikin sanya idanun da aka tura ƙasar, gabanin babban zaɓen ƙasar da za a yi a ranar 20 ga watan Disamba.

EU ta buƙaci hukumomin Congo haɗi da masu ruwa da tsaki, da su yi dukkan mai yuwuwa don ganin cewa al’ummar ƙasar sun gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana.

KU KUMA KARANTA: Somaliya ta shiga ƙungiyar ƙasashen gabashin Afirka

Ƙasar da ke tsakiyar Afirka mai ɗauke da mutane kusan miliyan 100, na shirin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, ‘yan majalisu na tarayya, wanda shugaba mai ci, Félix Tshisekedi, mai shekaru 60 ke neman wa’adi na biyu

Tshisekedi ya hau karagar mulkin ƙasar bayan lashe zaɓen da aka gudanar a shekarar 2018, wanda aka yi zargin an tabka maguɗi.

Sama da shekaru 30 na fama da tashe-tashen hankula na masu ɗauke da makamai daga gabashin ƙasar, wato inda aka jibge dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma na ƙungiyar ƙasashen gabashin Afirka.

A makon jiya ne, Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar da cewa ta sanya hannu kan yarjejeniyar janye dakarun wanzar da zaman lafiya 14,000 da ta jibge tun a shekarar 1999 a cikin ƙasar.

Leave a Reply