Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin 2024

0
180

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2024 ga zaman Majalisar Dokokin ƙasar nan a ranar Laraba cikin minti 25 kacal.

Shugaban ya fara gabatar da kasafin kuɗin ne da misalin karfe 11:40 na safe kuma ya kammala da misalin karfe 12:05.

KU KUMA KARANTA: Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin baɗi na N27.5tr ranar laraba

Yawanci shugabannin baya kan ɗauki lokaci mai tsawo suna gabatar da kasafin kuɗinsu ga majalisar dokokin ƙasar nan.

Ana sa ran shugaban zai tafi Dubai domin halartar wani taro a ranar Alhamis.

Leave a Reply