No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wasu ’yan ta’adda sun kashe wani basaraken gargajiya da wasu ’yan sanda biyu da wani farar hula ɗaya a mararrabar Ahiara da ke yankin Ahiazu na ƙaramar hukumar Mbaise da ke Jihar Imo.

Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da sabon kwamishinan ’yan sandan Jihar Imo, Danjuma Aboki, ya soma rangadi tare da jami’ansa a ƙaramar hukumar.

Aminiya ta samu cewa ajali ya katse hanzarin ’yan sanda ne a lokacin da suke bakin aiki sanye kakin ɗan sarki.

Haka kuma, bayanai sun ce ƙarar kwanan ce ta cimma farar hular wanda tsautsayi ya biyo da shi hanyar kuma aka yi rashin sa’a harsashi ya same shi.

KU KUMA KARANTA: An kashe mutane 2 da raunata 8 a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi

Shi kuwa basaraken gargajiyar da ya riga mu gidan gaskiya, shigar burtu ’yan ta’addan suka yi tamkar wasu baki masu kawo masa ziyara.

Kakakin ’yan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sun shiga farautar waɗanda suka aikata wannan mummunar ta’asa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...