An bankaɗo sabon shirin tayar da hargitsi a jihar Kano kan hukuncin tsige Gwamna Abba

0
136

Wata ƙungiyar goyon bayan APC ƙarƙashin inuwar ‘Progressive League of Youth Voters (PLYV)’, ta nuna damuwa cewa gwamnatin jihar Kano na shirya zanga-zanga don tayar da tarzoma a babban birnin jihar a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, rahoton Blueprint.

Hakan ya biyo bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na baya-bayan nan da ta tsige Gwamna Abba Yusuf daga kujerarsa. Legit Hausa ya wallafa.

A cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba, a Abuja, Audu Usman Shuaibu, shugaban ƙungiyar na ƙasa ya buƙaci hukumomin tsaro da su shiga lamarin sannan su kare mazauna Kano daga tashin hankali.

KU KUMA KARANTA: NNPP ta shigar da ƙara gaban Kotun Ƙoli kan shari’ar gwamnan Kano

Shuaibu ya yi zargin cewa an shirya zanga-zangar ne don tsoratar da kwamitin Kotun Koli da ke jagorantar ƙarar zaɓen gwamnan Kano da aka ɗaukaka, ta yadda za a juya hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke nasara ya koma wajensu.

Leave a Reply