An tsayar da ranar ci gaba da sauraron shari’ar ɗan China da Ummita

0
175

An tsayar da ranar da za a ci gaba da sauraren karar dan kasar Chinan nan Mista Frank Geng Quarong da ake zargi da kashe budurwarsa Ummulkusum Sani wadda aka fi sani da Ummita a Jihar Kano.

Babbar kotun jihar ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Aminu Ado Maaji ta sanya ranar 6 ga watan Disamba domin ci gaba da sauraren ƙarar.

A bara ce aka soma gurfanar da Mista Geng a gaban kotun da ke zamanta a Miller Road, inda ake tuhumarsa da zargin da laifin kisan kai wanda ya saɓa wa sashe na 221 na dokar penal code.

Kakakin babbar kotunan Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya ce an dakatar da shari’ar ce na tsawon watanni takwas saboda alkalin da ke jiɓintar shari’ar na cikin kwamitin alkalan da ke jagorantar shari’ar kotun sauraron ƙararrakin zaɓen da aka gudana a bana.

KU KUMA KARANTA: Mr Geng ya musanta zargin kashe Ummita a Kano

Ana iya tuna cewa, Mista Frank Geng Quarong, wanda ya gurfana a gaban Babbar Kotun jihar Kano kan zargin kisan masoyiyarsa, Ummukulsum Sani Buhari, ya tabbatar da kashe ta da wuka.

Yayin da ake tuhumar wanda ake zargin ya shaida wa lauyan masu ƙara, Barista Aisha Mahmud cewa ya zo Najeriya ne a shekarar 2019, kuma yana aiki da Kamfanin Tufafi na BBY inda yake karɓar albashin naira miliyan 1.5 duk wata.

Mista Quarong ya shaida wa kotun cewa ya kashe wa marigayiya Ummita sama da N60m a lokacin da suke sharɓar romon soyayya.

Aminiya ta ruwaito, rahoton kisan Ummita ya bulla ne tun a bara, inda ake zargin a ranar 17 ga watan Satumbar baran ce Mista Quarong ya kashe masoyiyarsa a gidansu da Unguwar Janbullo daura da unguwar Kuntau da ke yankin Dorayi a ƙaramar hukumar Gwale ta Jihar Kano.

Leave a Reply