An kashe mutane 2 da raunata 8 a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi

Mutane 2 ne suka mutu yayinda wasu 8 suka jikkata a wani rikici tsakanin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Suru ta jihar Kebbi, Daily trust ta wallafa.

Shugaban ƙaramar hukumar Suru, Mohammed Lawal, wanda ya bayyana hakan a jiya a lokacin da yake zantawa da gwamna Nasiru Idris, ya bayyana cewa rikicin ya faro ne da safiyar ranar asabar, inda wasu manoma suka je gonakinsu suka haɗu da makiyaya da shanunsu a gonakin.

Ya ce, “manoman sun tambayi makiyayan ko su ne suke lalata amfanin gonakinsu wanda hakan ya haifar da rikici a tsakaninsu.  An kashe mutane, an lalata dukiyoyi da gidaje.”

KU KUMA KARANTA: Rikicin manoma da makiyaya ya yi ajalin mutum 12 a Taraba

Ya ce ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Kankure, Tunga Rimi, Tunga Mai Rakumi, Runhewan Dulmeru, Sabuwan Kendawa da Limarein.

Mai magana da yawun gwamnan, Ahmed Idris, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce Gwamnan ya umurci Shugaban Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Bello Rilisco, da ya zaƙulo waɗanda abin ya shafa tare da tallafa musu da kayayyakin abinci da sauran kayayyakin agaji.

Ya ce, “Gwamna Nasiru ya kutsa kai cikin rikicin manoma da makiyaya a yankin Suru da Koko Besse na jihar domin dawo da zaman lafiya mai dorewa a cikin al’ummomin da rikicin ya shafa.

“Ya kuma bayar da gudummawar N13m ga iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka samu raunuka a rikicin.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *