Nijar ta soma amfani da tashar samar da hasken lantarki ta sola mafi girma domin cike giɓin lantarki da ƙasar ke fuskanta bayan Najeriya ta hana ta wuta saboda juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yuli, kamar yadda Ministan Ma’aikatar Makamashi na ƙasar ya bayyana ranar Lahadi.
A wani jawabi da ya yi a gidan talabijin, Mahaman Moustapha Barke ya ce tashar ta soma aiki ne ranar 15 ga watan Nuwamba.
Tashar ta sola tana da fayafayan sola fiye da 55,000 waɗanda za su iya samar da megawat 30 na hasken lantarki, in ji shi.
Minista Barke ya ƙara da cewa tuni kamfanin samar da hasken lantarki na Nijar Nigelec ya tabbatar da “samun inganci na hasken lantarki” a Yamai babban birnin ƙasar da kuma biranen Dosso da Tillaberi.
KU KUMA KARANTA: Sojoji sun roƙi kotun ECOWAS ta tilasta wa makwabtan Nijar ɗage takunkumai
Ranar 25 ga watan Agusta aka so ƙaddamar da tashar sai dai an samu jinkiri ne saboda wasu ƙwararrun ma’aikatan da ke kula da ita sun daina aiki bayan juyin mulkin da aka yi a ƙasar, in ji Barke.
Ya ƙara da cewa sauran ma’aikatan da ba su tafi ba ne suka tabbatar da wannan shiri ya soma aiki.
Ofishin jakadancin Fasansa a Nijar ya yi gargaɗi cewa akwai yiwuwar “fuskantar hatsari” saboda “ba a kammala tashar kamar yadda aka tsara ba.”
An kashe kusan CFA biliyan 20 (kwatankwacin $33m) wajen gina tashar, kuma an karɓi akasarin kuɗin ne daga cibiyoyin bayar da rance na Faransa da kuma tallafin Tarayyar Turai.
Nijar na fama da yawan ɗaukewar hasken lantarki bayan Najeriya, wadda ita ce take ba ta yawancin lantarkin da take amfani da shi, ta hana ta a wani mataki na jerin takunkuman da ƙungiyar ECOWAS ta sanya wa ƙasar saboda juyin mulkin da sojoji suka yi ranar 26 ga watan Yuli.
Ƙasar Nijar na da wadataccen haske rana, wanda masana ke cewa zai iya samar mata da lantarkin da take buƙata har ma ta bai wa wasu ƙasashen.